logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Guinea Bissau da ministar harkokin wajen kasar sun halarci bikin mika tallafin abinci na gaggawa

2023-03-15 13:57:23 CMG Hausa

An gudanar da bikin mika shinkafa da gwamnatin kasar Sin ta samar a matsayin tallafin gaggawa ga kasar Guinea Bissau a ranar 13 ga watan. Jakadan Sin dake Guinea Bissau Guo Ce da ministar harkokin wajen kasar Guinea Bissau Suzi Carla Barbosa sun halarci bikin tare. 

Guo Ce ya ce, tallafin na daga cikin tallafin abinci na gaggawa da gwamnatin kasar Sin ta ba kasashen Afirka da dama, ciki har da tan 1,062 na shinkafa ga kasar Guinea-Bissau. 

Yayin da ake fuskantar matsalar karancin abinci a duniya a halin yanzu, kasar Sin na son daukar kwararan matakai don taimakawa kasashe masu tasowa wajen shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta fuskar samar da abinci. Ana kyautata zaton tallafin shinkafar zai taimakawa kasar Guinea-Bissau wajen magance matsalolin karancin abinci da jama'a ke fuskanta.

A nata jawabin, Madam Barbosa ya mika godiya ga gwamnatin kasar Sin bisa wannan agajin gaggawa na abinci da ta samarwa Guinea-Bissau, A matsaynsu na abokai da kuma ‘yan uwa na kwarai, samar da wannan tallafin abinci ga kasar Guinea Bissau wani mataki ne na aika sako a kan lokaci, wanda ke nuna cikakkiyar ruhin jin kai da zurfafa abokantaka da Guinea Bissau. (Safiyah Ma)