Kamfanoni masu zaman kansu dake Sin za su more yanayi mai kyau da fadada damar samun ci gaba
2023-03-13 15:57:00 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, kamfanoni masu zaman kansu dake kasar Sin, za su more yanayi mai kyau da kuma babbar dama ta samun ci gaba.
Li ya fadawa taron manema labarai cewa, gwamnati za ta kara zage damtse wajen samar da yanayin kasuwanci mai dogaro da kasuwa, bisa tsarin doka da kuma kasa da kasa, da kula da dukkan nau’o’in kamfanoni ba tare da nuna wani bambanci ba, da kare ’yancin mallakar kamfanoni da hakkoki da muradun ’yan kasuwa bisa doka.
Li ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da daidaito ga kowane nau'in kasuwanci, da kara tallafawa kamfanoni masu zaman kansu, wajen bunkasa harkokinsu na kasuwanci. (Ibrahim Yaya)