logo

HAUSA

Xi Jinping: Za a yi kokarin zamanintar da harkokin tsaron kasa da ma rundunar sojan kasar Sin

2023-03-13 10:48:01 CMG Hausa

A yau ne aka rufe taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a birnin Beijing, majalisar da ta kasance hukumar koli ta kasar. A jawabin da ya gabatar a yayin rufe taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, za a yi kokarin zamanintar da harkokin tsaron kasa da ma rundunar sojan kasar, ta yadda rundunar sojan kasar za ta taka rawar da ta kamata wajen kare ikon mulkin kai da tsaro da moriyar ci gaba na kasar. (Lubabatu)