logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta amince da sabbin mambobin majalisar gudanarwar kasar

2023-03-12 16:44:05 CMG Hausa

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, wadda ke zaman majalisar dokoki ta kasar, ta amince da sabbin 'yan majalisar gudanarwar kasar ko kuma majalisar ministoci, yayin zamanta na shekara dake gudana yanzu haka.

Bayan gabatar da sunayensu da Firaminista Li Qiang ya yi, mataimakan firaminista da ministoci da gwamnan babban banki da babban mai binciken harkokin kudi da sakatare janar na majalisar gudanarwa ta kasar, sun samu amincewa daga mambobin majalisar NPC na 14, a yayin zamansu na 5, na taronsu na shekara dake gudana.

Tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rattaba hannu kan umarnin nada wadannan jami'ai.

'Yan majalisar NPC sun kuma amince da zaben shugabanni da mataimaka da mambobi 8 na kwamitin musammam na majalisar NPC karo na 14.

Mataimakan firaministan da mambobi da sakatare janar na majalisar gudanarwar kasar, sun sha rantsuwar biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar. (Fa'iza)