logo

HAUSA

AU ta yi kira da karin mata su shiga a dama da su a fagen kimiyya da fasaha

2023-03-09 13:33:42 CMG Hausa

Shugaban hukumar Tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat ya yi kira ga karin mata da ’yan mata su shiga a dama da su a bangaren kimiyya da fasaha.

Moussa Mahamat ya bayyana haka ne jiya Laraba, albarkacin ranar mata ta duniya. AU ta yi wa ranar ta bana taken, “Fasahohi ga kowa: -kirkire-kirkire da fasaha domin daidaiton jinsi--shekaru 20 da ayyana yarjejeniyar Maputo”.

A cewarsa, taken ya dace da muhimman batutuwan da AU ke mayar da hankali kansu, na fadada samar da damar cin gajiyar fasahohin sadarwa ga mata, a matsayin wata hanya ta bayar da gudunmawa ga ci gaba mai dorewa ga harkokin mata, ta hanyar tabbatar da daidaiton jinsi da kara adadinsu a bangaren kimiyya da fasaha.

Ya ce Ranar Mata Ta Duniya ta bana, na zuwa ne yayin da nahiyar Afrika ke cika shekaru 20 da cimma yarjejeniyar ka’idojin kare hakkokin bil adama da hakkokin mata a Afrika, wanda aka fi sani da Maputo Protocol.

Ya ce a bayyane yake cewa, kirkire-kirkire da fasaha na da muhimmanci wajen ingiza ci gaban nahiyar Afrika, musamman ta hanyar gudunmawar da mata suka bayar, kuma suke bayarwa a yanzu a wannan bangare. (Fa’iza Mustapha)