logo

HAUSA

Ministan kudin Habasha ya yaba da kokarin Sin kan ci gaban kasa mai inganci

2023-03-09 09:51:14 CMG Hausa

Ministan kudin kasar Habasha Ahmed Sid, ya bayyana cewa, kokarin da kasar Sin ke yi kan ci gaba mai inganci ya ingiza ci gaban kasar, da ma duk duniya baki daya.

Da yake zantawa da wikilin CMG a jiya, Ahmed Sid ya ce, ci gaba mai inganci, tunani ne mai kyau, saboda ya hada ci gaba a fannonin kirkire-kirkiren fasahohi, da hakuri da bambancin ra’ayi, da kare muhalli, da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa. Kana, ci gaba mai inganci zai samar da muhallin rayuwa mai dorewa ga miliyoyin al’umma.

Ya kara da cewa, ba al’ummun Sinawa ne kadai za su ci gajiya daga ci gaba mai inganci na kasar ba, har ma da na duniya baki daya, domin zai ingiza bunkasuwar duk duniya ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ciki har da kasashen Afirka.

A cewar ministan, suna mai da hankali matuka kan taruka biyu na kasar Sin na bana, musamman ma kan batutuwan da suka shafi hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Jamila)