logo

HAUSA

A kalla mutane 7 ne suka gamu da ajalinsu 84 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da motar bas a Najeriya

2023-03-09 19:57:13 CMG Hausa

 

      

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa, a kalla mutane 7 ne suka mutu, yayin da wasu 84 kuma suka ji raunuka, a wani hatsarin da wata motar bas ta yi taho mu gama da jirgin kasa a Lagos Alhamis din nan.

Jami’in hukumar mai kula da yankin Ibrahim Farinloye ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, motar bas din mai dauke da ma’aikatan gwamnatin jihar na kokarin tsallaka layin dogo ne, a lokacin da jirgin kasan da ke shigowa Lagos daga Abeokuta ya markade motar a kan titin jirgin. Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani.

Farinloye ya kara da cewa, duk wadanda suka jikkata suna samun kulawar da ta kamata a asibitoci daban-daban.(Ibrahim)