logo

HAUSA

An kashe mutane a kalla 11 a Burkina Faso

2023-03-07 10:07:42 CMG Hausa

Mutane a kalla 11 ne suka mutu, ciki har da sojoji da fararen hula masu taimaka musu, yayin wani harin kwantan bauna da aka kai wani sansanin soji dake arewa maso yammacin Burkina Faso, a ranar Asabar.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa Xinhua cewa, wasu mutane dauke da makamai ne suka kai hari kan sansanin soji a kauyen Zaba dake lardin Nayala na arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji 11 da fararen hula masu taimaka musu.

Majiyar ta kara da cewa, harin ya kuma jikkata wasu sojojin da fararen hula. Tana mai cewa an kuma hallaka ’yan ta’adda wajen 20 wadanda suka kai harin.

Kamfanin dillancin labarai na kasar AIB, ya ruwaito a jiya Litinin cewa, an kashe gomman ’yan ta’adda cikinsu har da shugabanni a ranar Lahadi, yayin wani hari ta sama da aka kai musu a yankin gabashi da arewa maso tsakiyar Burkina Faso. (Faeza Mustapha)