logo

HAUSA

Tafarkin Sin Na Zamanantar Da Kanta Zai Amfani Kasashe Masu Tasowa

2023-03-05 12:00:32 CMG Hausa

Wani manazarci a kasar Afrika ta Kudu, David Monyae ya ce, yayin da kasar Sin ta kama sabuwar hanyar gina kasa ta zamani bisa tsarin gurguzu ta hanyar zamanintar da kanta, ya kamata kasashe masu tasowa na Afrika da sauran sassan duniya, su yi amfani da damar da Sin ta samar, ta zamanantar da kansu bisa yanayinsu na cikin gida.

David Monyae wanda shi ne daraktan cibiyar nazarin harkokin Afrika da Sin ta jami’ ar Johannesburg, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu na karfin tattalin arziki a duniya, ya sauya dadadden ra’ayin da ake da shi cewa, hanyar zamanintarwa ta yammacin duniya ita ce daidaitacciyar hanyar samun ci gaba a duniya.

Ya ce, zamanintarwa irin ta kasar Sin na da damar karfafawa da yin tasiri a sauran sassan duniya, musamman tsakanin kasashe masu tasowa.

Ya kara da cewa, nasarorin da Sin ta samu a baya-bayan nan wajen fatattakar talauci da samun ci gaban tattalin arziki, sun burge shi.

Da yake bayyana nasarar da Sin ta samu na fatattakar talauci a matsayin nasara ta bai daya ga duniya maimakon nata ita kadai, David Monyae ya kara da cewa, kasar Sin ta cimma muradi na farko cikin muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030, shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara.

Har ila yau, ya ce ya kamata kasashe masu tasowa su samu kwarin gwiwa tare da zamanantar da kansu ta hanyar da ta dace da yanayi da tarihi da zaman takewa da tsarin tattalin arzikinsu. (Fa’iza)