logo

HAUSA

Masana a Najeriya sun fara hasashe kan manufofin sabuwar gwamnati ta fuskar tattalin arziki da diplomasiyya

2023-03-04 14:51:17 CMG Hausa

Tun bayan sanar da Bola Tinubu a matsayin mutumin da ya samu nasara a zaben shugaban tarayyar Najeriya, al’ummar kasar suka fara tattaunawa kan abubuwan da ake kyautata zaton sabon shugaban zai gudanar da zarar ya fara aiki.

Najeriya dai tana fuskantar kalubale da dama kama daga batun tattalin arziki , tsaro da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

Wakilinmu daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya tattauna da wasu masana a bangaren tattalin arziki da diplomasiyya ga kuma rahoton daya aiko mana.///

Najeriya wadda ake yi wa lakabi da uwar Afrika, ta yi shuhura a fannoni da dama kama daga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewa, sai dai kuma tsakanin shekaru sama da goma da suka gabata kasar ta fuskanci kalubale da dama wadanda suka haifar da cikas wajen ci gaban wasu daga cikin muradun ta.

Batun rashin tsaro da karancin aiki yi, kana da koma bayan bangarorin tattalin arzikin cikin gida sun kasance manya abin dubawa ga sabon shugaban kasar.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka malami ne a sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Bayero dake Kano a arewacin Najeriya, ya ce, abin da ya kamata sabon shugaban kasar ya fara mayar da hankali a kai dai shi ne kyautata alakar Najeriya da kasar Sin, domin kamar yadda ya ce yanzu kaso 90 na kayayyakin da ake amfani da su a tarayyar Najeriya suna fitowa ne daga kasar China.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce zai iya tunawa akwai lokacin da shugaban Muhammadu Buhari ya yi alkawarin amfani da kudin kasar Sin cikin asusun ajiyar Najeriya dake kasashen waje domin rage dogaro a kan Dala da Yuro wanda hakan zai saukawa ’yan kasuwar Najeriya dake fita sayo kaya zuwa kasar ta China inda aka yi kiyasin cewa sun kai kaso 70.

A don haka yana fatan sabon shugaban Bola Ahmad Tinubu zai sake dauko maganar domin aiwatarwa.

“Wannan abu ne wanda a wancan lokaci muke taya murnar cewa zai taimakawa ’yan kasuwarmu wajen maganin asarar da suke yi ta musayar kudade, ita Dala a Najeriya ba kudin da ya fi ta daraja, ita kuma dala a China ba ta da wata daraja saboda su ’yan kasar ta Sin suke kishin kasarsu, suna da kishin kudin su. Idan ka sa ka canja Naira a cikin tsada, ka tafi can Sin, kuma dala ba ta da wata daraja, ka karya ta, ’yan kasuwar Najeriya suna asara. Wannan tsari ne da shugaban kasa ya dauko tsari ne wanda zai kyautu, amma daga karshe a ce ya mutu.”

Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ci gaba da cewa idan har sabon shugaban kasa ta Najeriya zai nemi shawararsa kan alakar kasar Sin da Najeriya, shawarar da zai fara ba shi dai shi ne ya sake maido da waccan manufa domin zartar da ita. Don canja wani kaso na kudin ajiyar Najeriya dake waje zuwa Yuan na kasar Sin zai rage karfin dala a Najeriya, sannan kuma ’yan kasuwarmu za su samu saukin gudanar da harkokin cinikayyar su.

Ta fuskar sha’anin diplomasiyya da kasashen ketare kuwa na tambayi Dr Isma’il Mohammed malami a kwalejin share fagen shiga jami’a dake jihar Kano ko wane sauyi yake jin za a samu a sabuwar gwamnatin da za a kafa a Najeriya.

“Mu kasarmu ta Najeriya har yanzu a kasashen Afrika cikin Afirka ne muke da bakin magana kuma muke da ta cewa, amma sabanin Afirka in ka tsallaka kamar kasashen Asiya, su China da Turai din za ka ga cewa kusan duk matsayin da gwamnatin Najeriya suke dauka tun daga 1999 har zuwa yanzu za ka ga duk manufofi daya ne na manufofin harkokin kasar waje.”

Ko da yake ya ce komai zai iya sauyawa, musaman ma ganin yadda Najeriya ke kara samun tagomashi a tsakanin manyan kasashen duniya bisa la’akari da arzikin da take da shi idan aka kwatanta da sauran kasashen dake nahiyar. (Garba Abdullahi Bagwai)