logo

HAUSA

Mataimakiyar sakatare-janar MDD ta kai ziyarar gani da ido a makarantar faramare “Pays-Bas” da ke Yamai

2023-03-03 10:24:51 CRI

 

Shekaru biyu ke nan da abkuwar gobara da tashi a yammacin ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2021, da ta halaka yara 21 da lalata azuzuwan zana da dama a makarantar  “Ecole Pas-Bas” dake Yamai. Tun daga wannan lokaci ne, gwamnatin Nijar ta dauki niyyar kawar da azuzuwan zana a makarantun faramare musamman ma a makarantun renon yara, tare da tallafin MDD ta hanyar kungiyar UNICEF wajen sake gina sabuwar makaranta domin sauran yaran makarantar “Ecole Pays-Bas”. Dalilin ke nan, madam Amina Mohamed ta kai ziyara wannan makaranta domin ganewa idonta kokarin da hukumarta ta yi domin kyautata yanayin karantun yaran wannan makaranta.

Tare da rakiyar jami’an MDD da na kungiyar UNICEF, da mambobin gwamnatin Nijar da kuma hukumomin ilimi, mataimakiyar sakatare-janar MDD, Amina Mohamed ta kai ziyarar gani da ido. Na fara da tambayarta makasudin wannan ziyara.

“Wannan ziyarar da muka zo, wato duk abin da aka fada a Turance a can majalisar dunkin duniya, shi muke so mu zo mu gani anya ko ana yi ne ko ba a yi, ana tallafawa gwmnati ko ba a yi. Duk abin da ya faru, da gobarar nan da aka yi, da aka rasa yaran nan 21, bai kamata a ce an yi rashi haka kawai ba, a’a, wannan makaranta a sake gina ta.”

Kuma babbar jami’ar ta MDD ta bayyana gamsuwarta kan abin da idonta suka gani.

“Mun gamsu amma ba nan ta kare ba, don sauran jama’a ya kamata su gani, su marawa gwamnati baya, su ma su dauka nasu ne, a ci gaba da shi don a samu a kara.”

Game da batun ilimi a Nijar, na tambaye ta yaya ganin tafiyar ilimi tare da zamani. Sai ta ce da ni.

“To ai idan ba a bi shi ba, za a bar mu baya, mu kuma ba za a bar mu baya ba. Don duk abin da ka baiwa dan Afrika, ka ba dan Nijar, ka ba dan Gana, idan ka ba shi dai abin da aka ba bature ai zai fi shi. Saboda haka mu, ba za a bar mu a baya ba. Duk abin da ake kawowa, a kawowa mata, a kawowa maza, kowa a hada hannu, a hada gwiwa a ci gaba.”

Daga karshe, na kuma tambaye ta, ko yaya take ganin ci gaban ilimi a Nijar.

“Ai ba shakka shugaban naku, ba abin da yake magana illa ilimi, da inda jama’a za su samu. Kuma yana maganar mata kullum, kullum shi maganarsa ke nan. Mu kuma mun ce ya kamata mu mara masa baya, mun ga mutumin da ya ce zuciyarsa daya, kuma ga abin da yake so ma mutanen shi, ya kamata mu mara masa baya, shi za mu yi, yana ganin illimin ne shi zai tada kasar nan.”

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.