logo

HAUSA

Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin taron BRICS a karshen watan Agusta

2023-03-03 13:42:59 CMG Hausa

Minista a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu, Mondli Gungubele, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasarsa za ta karbi bakuncin taron kolin kungiyar BRICS a lardin Gauteng na kasar tsakanin ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta mai zuwa.

Mista Gungubele ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da yake gabatar da bayanai dangane da taron majalisar ministocin kasar ga manema labaru.

A cewarsa, babban taken taron kolin kungiyar BRICS na wannan karo, shi ne “kasashen BRICS da nahiyar Afirka: abokantaka don gaggauta samun karuwar tattalin arziki, da ci gaba mai dorewa, da ra’ayin baiwa kowa ikon fada-a-ji”.

Mambobin kungiyar BRICS sun hada da kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, gami da Afirka ta Kudu. A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2023, kasar Afirka ta Kudu ta karbi kujerar shugabancin kungiyar BRICS ta karba-karba daga hannun kasar Sin. (Bello Wang)