logo

HAUSA

Dabaru daga nahiyar Afrika na da muhimmanci wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa

2023-03-02 11:36:38 CMG Hausa

Mataimakiyar sakatare-janar na MDD Amina Mohammed, ta bayyana dabarun da Afrika za ta bullo da su a matsayin muhimmai wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Amina Mohammed ta bayyana haka ne lokacin da take jawabi ga zama na 9 na nahiyar Afrika game da muradun ci gaba masu dorewa, wanda ke gudana daga 28 ga watan Fabreru zuwa yau, 2 ga wata, a zahiri da kuma kafar intanet, a birnin Niamey na jamhuriya Niger.

Wata sanarwar da hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA) ta fitar, ta ruwaito jami’ar na yin kira da a kara kyautata kudurin shugabanci da jajircewa da kuma zuba jari wajen cimma muradun a Afrika.

Ta ce akwai fahimta ta bai daya cewa, ta hanyar dabarun da aka bullo da su a Afrika, za a iya sauya alkibla da shawo kan kalubalen da ake fuskanta na cimma ajandar shekarar 2063 da muradun ci gaba masu dorewa. 

Ta kara da cewa, dole ne shugabannin duniya su dauki burikan rage talauci da rashin daidaito zuwa shekarar 2030, kuma dole ne su yi hakan ta hanyar zuba jari a Afrika, wato zuba jari a kasashen nahiyar da ma harkokin da suka shafi jama’a, musammam mata da matasa. (Fa’iza Mustapha)