Kwamitin kolin JKS ya gudanar da taron tuntuba kan shirin yi wa sassan jam’iyyar da hukumomin gwamnati garambawul
2023-02-28 21:51:14 CMG Hausa
Kwamitin koli na JKS, ya gudanar da wani taron tuntuba a yau Talata, domin jin ra’ayoyi tare da sanar da shirin da ake da shi na yi wa sassan JKS da hukumomin gwmnati garambawul, ga sauran jam’iyyun siyasa da ba na JKS ba, da kungiyar masana’antu da ciniki ta kasar da mutanen da ba su da alaka da wata jam’iyya.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar sojan kasar, shi ne ya jagoranci taron, inda kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi.