logo

HAUSA

Hukumar INEC ta fara karbar sakamakon zaben shugaban kasa a birnin Abuja

2023-02-27 10:37:02 CMG Hausa

A ranar Lahadi 26 ga wata, shugaban hukumar zaben Najeriya farfesa Mahmud Yakubu ya bude cibiyar karbar sakamakon zaben shugaban kasa daga jahohi, a matsayinsa na babban baturen zabe na kasa.

An bude cibiyar ce a harabar babban dakin taro na kasa da kasa dake birnin Abuja, inda ya ce cibiyar za ta kasance dandalin karba da kuma sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka tattaro daga jahohin kasar bayan kammala zaben a ranar 25 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

A jawabinsa yayin bude cibiyar, shugaban hukumar zaben ya ce an raba tsarin karbar sakamakon ne zuwa kashi hudu, na farko za a fara da mazabu 8,889 dake kasar sai kuma a shiga kananan hukumomi 774 daga nan kuma turawan zabe na jahohi ciki har da birnin Abuja su karba kafin daga bisani su gabatar da sakamakon da kowanne dan takara ya samu zuwa ga wannan cibiyar dake Abuja.

“Cibiyar za ta rinka kasancewa a bude a kowane lokaci dare da rana sai dai hutu na ’yan mintuna wanda a matsayina na baturen zabe, ni ne nake da hakkin sanar da tafiya hutun shan ruwa.”

Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da cewa ’yan takarar shugabancin kasa 18 ne suka fafata a zaben na ranar Asabar, to amma wadanda suka fi suna a cewar mashaharanta su ne guda 4 da suka tsaya karkashin jam’iyyun Labour Party, NNPP, PDP da APC, biyu daga cikin ’yan takarar sun fito ne daga shiyyar kudancin Najeriya yayin da ragowar biyun suka fito daga arewacin kasar.

Kamar yadda shugaban hukumar zaben ya tabbatar, mutane miliyan 87.2 ne suka karbi katin zabe kuma suka gudanar da zaben.

Sakamakon zaben jihar Ekiti ne shugaban hukumar zaben ta kasa ya fara sanarwa a farkon zaman na jiya Lahadi, bayan da babban jami’in tattara sakamakon zaben jihar farfesa Akeem Lasisi ya gabatar masa inda dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 201,494 sai mai biye masa na PDP da kuri’u dubu 89,554 sai na jam’iyyar Labour Party wanda ya samu kuri’u dubu 11,397 yayin da jam`iyyar NNPP ta samu kuri’u 264.

Bayan sanar da wannan sakamako ne, shugaban hukumar zaben ta tarayyar Najeriya ya yi kira ga ’yan jaridu da kungiyoyin sa ido da kuma wakilan jam’iyyu kamar haka.

“Za a rinka haska ainihin sakamakon zaben a allunan talabijin da aka samar a kowane kusurwa dake cikin wannan daki, a don haka ina kira ga dukkannin wakilan jam’iyyu da ’yan jaridu da su rinka amfani da sakamakon da ake nunawa a cikin wadannan allunan talabijin a matsayin sakamakon da aka fitar a hukumance.”

Hukumar zaben dai za ta ci gaba da karbar sakamakon zaben shugaban kasar a wannan rana ta Litinin 27 ga wata.

Tun dai daga jiya Lahadi 26 ga wata ofisoshin hukumar zabe ta kasa dake jahohi suka fara fitar da sakamakon zaben sanatoci da na ’yan majalissar wakilai. (Garba Abdullahi Bagwai)