logo

HAUSA

Sin za ta inganta tsarin ba da hidimar jiyya ta likitancin gargajiya na kasar

2023-02-27 14:19:36 CMG HAUSA

 

Hukumar sa ido kan ayyukan kiwon lafiya ta kasar Sin, ta ce kasar za ta dauki matakin inganta tsarin ba da hidimar jiyya ta likitancin gargajiya na kasar, ta yadda za a kara karfin samarwa al’umma hidimar jiyya ta gargajiya a wurare daban-daban.

Hukumar mai kula da ayyukan likitanci da magungunan gargajiya ta kasar Sin ta kira wani taro a jiya, wanda ya samu halartar shugabannin hukumomi masu ruwa da tsaki, inda aka bayyana cewa, kasar Sin za ta kafa wasu cibiyoyin jiyya na likitancin gargajiya na kasar a yankin Xiong’an, tare da ingiza aikin gina cibiyar likitanci da magungunan gargajiya ta Sin.

Taron ya kuma bayyana cewa, za a gabatar da ma’aunin da za a bi a wannan fanni, don ingiza kafa cibiyoyin likitancin gargajiya a cikin al’umma. Baya ga haka, za a kara karfin horar da masu ba da jiyya a wannan fanni.

Kazalika, Sin ta yi alkawarin tsai da ma’auni da jadawalin ba da jiyya dangane a wannan fanni, ta yadda za a kara karfin hidimtawa al’ummun kananan kabilu.  (Amina Xu)