logo

HAUSA

An kammala kada kuri’a a babban zaben kasa da zaben ‘yan majalisar dokokin tarayyar Najeriya

2023-02-26 16:41:33 CMG Hausa

An gudanar da babban zaben kasa gami da na ‘yan majalisar dokoki a tarayyar Najeriya a jiya Asabar, inda al’ummar kasar suka nufi mazabu daban-daban a fadin kasar domin kada kuri’unsu. Wannan shi ne karo na farko tun shekara ta 2011, da aka gudanar da babban zaben kasar bisa lokacin da aka tsara, ba tare da dagewa ba.

A wannan karo, gwamnatin Najeriya ta shigo da wasu sabbin fasahohi domin shawo kan matsalar magudin zabe da kawar da takaddama, ciki har da tantance matsayin masu kada kuri’a har sau biyu, wato baya ga tantance katin zabe, akwai bukatar tantance zanen yatsa ko fuskar mai kada kuri’a, don tabbatar da cancantar sa.

Da yammacin jiya Asabar, bayan kammala kada kuri’u a mazabu daban-daban, aka fara kirga kuri’un karkashin sa idon wakilan jam’iyyun siyasar kasar gami da masu sa ido. (Murtala Zhang)