logo

HAUSA

Sakamakon farmaki da aka kai kan kayanta, hukumar INEC ta dage zabe a wasu akwatuna zuwa Lahadi 26 ga wata

2023-02-26 15:11:36 CMG Hausa

A ranar Asabar 25 ga wata, shugaban hukumar zaben Najeriya farfesa Mahmud Yakubu ya kara tabbatar da kudirin hukumar na kaiwa ga karshen zabukan da ta sanya a gaba, duk kuwa da barazanar da ’yan ta`adda suka kaiwa  kayayyakinta a wasu runfunan zabe jiya Asabar.

Farfessa Mahmud Yakubu ya furta hakan ne yayin ganawa da manema labarai jiya a birnin Abuja, inda ya ce sun samu rahotanni daga sassa daban daban na kasar na farmaki da aka kai wasu runfunan zabe a daidai lokacin da jama’a ke tsaka da gudanar da zabe.

Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaban hukumar zaben ta tarayyar Najeriya ya ce har yanzu hukumar tana da kwarin gwiwar samun nasarar zabukan, sakamakon irin goyon bayan da take samu daga hukumomin tsaron  kasar.

Ya ce farfasa wasu akwatinan zaben da aka yi a wasu jahohin a ranar Asabar abin takaici ne matuka. Lamarin da ya tilasta wa hukumar dage ci gaba da zaben zuwa ranar Lahadin nan.

Farfesa Mahmud Yakubu ya ce akwatina 141 ne dage zaben ya shafa a jihar Bayelsa bayan samun rahotannin tashin rikicin da ake zargin wasu ’yan bangar siyasa da aikatawa.

Ya ce bayan wadannan rahotanni ne jami’an tsaro suka yi kokarin maido da zaman lafiya a wuraren.

Shugaban hukumar zaben ya ci gaba da cewa dukkannin dalubai masu yiwa kasa hidima da suke gudanar da aikin a wuraren da aka kaiwa hari sun amince za su koma bakin aiki.

Farfessa Mahmud Yakubu ya kara da cewa hukumar ta gamsu sosai bisa yadda aka yi amfani da na’urar tantance masu zabe, wanda wannan shi ne karo na farko a tarihin zaben Najeriya da aka yi amfani da wannan na`ura da ake kira da BVAS.

“Hakika mun yi asarar akwatinan jefa kuri’a a wasu wurare, amma wannan ba shi ne manufar wadannan ’yan ta’adda ba, burin su dai a nan shi ne su sace ko kuma lalata wadannan na’urori, amma dai za mu ci gaba da kokarin kare wadannan kayayyaki, domin kamar yadda muka samu rahoto jami’an tsaron da suke aiki da hukumar sun samu nasarar kame wasu daga cikin  wadannan ’yan bangar siyasa, inda suka kwato uku daga cikin na’urar BVAS 6  da suka sace.”

“Kar ku manta za mu sake amfani da wannan na’ura ta BVAS a ragowar zabukan dake tafe nan da makonni biyu wato a zaben gwamna da na ’yan majalissar dokoki, sabo da haka ba za mu yi wasa da wadannan na’urori ba domin suna da matukar mahimmanci wajen tabbtar da sahihin zabe.”

Shugaban hukumar zabe ta tarayyar Najeriya ya sanar da cewa a wannan rana ta Lahadi 26 ga wata hukumar za ta fara tattarawa tare kuma da sanar da alkaluman jahohi na sakamakon zaben shugaban kasa, aikin tattara sakamakon da ake ganin zai iya kaiwa gobe Litinin 27 ga wata kafin a kai ga karkarewa. (Garba Abdullahi Bagwai)