logo

HAUSA

‘Yan Najeriya sun fara zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun Tarayya

2023-02-25 18:29:17 CRI

 

Yau Asabar 25 ga watan Fabarairu ne, ‘yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a suka doshi rumfunan zabe, don zaben sabon shugaban kasa da na ‘yan majalisun dattajai da na wakilai, a kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

Daga nan dakin mu na watsa shirye-shirye dake birnin Beijing, na tuntubi wakilinmu dake Tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai don jin yadda zaben ke gudana. Sai dai na fara tambayarsa ne kan matakan tsaron da aka dauka don ganin an gudanar da wannan zabe cikin lumana.