Kwamitin kolin JKS karo na 20 zai yi cikakken zama karo na 2
2023-02-21 19:18:38 CMG Hausa
Bisa shawarar da aka yanke a taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Talatar nan, za a gudanar da cikakken zama karo na biyu na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 daga ranar 26 zuwa 28 ga watan Fabrairun da muke ciki a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. (Ibrahim)