logo

HAUSA

Najeriya za ta kashe Naire biliyan 28 wajen ayyukan inganta hasken wutan lantarki

2023-02-16 09:24:40 CMG Hausa

A ranar Laraba 15 ga wata, majalissar ministocin Najeriya ta amince da kashe Naira biliyan 28 wajen aiyukan inganta sha’anin wutan lantarki a kasar.

Yayin taron wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, an ce, za a yi amfani da Naira biliyan 26.6 wajen sake wayoyin da suke dakon wuta zuwa tasoshin rarraba wuta wanda tsayin su ya kai kilomita 1,022 yayin da kuma za a kashe Naira biliyan 1.4 wajen odar mayan na’urorin rarraba wuta guda 20.

Ministan wutan lantarki na tarayyar Najeriya Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labaru jim kadan bayan kammala taron majalissar zartarwa ta tarayyar a birnin Abuja.

Ya ce aikin sake wayoyin dakon wutar ya zama wajibi saboda wanda ake amfani da su yanzu haka sun tsufa sosai kuma karfin su ya ragu ba za su iya daukar karfin wutar da ake kokarin samarwa ba.

Ministan ya ce aikin sauya wayoyin zai shafi dukkan sassan kasar ne. (Garba Abdullahi Bagwai)