logo

HAUSA

Najeriya za ta fara amfani da na’urar sanya ido kan jiragen ruwa na dakon kaya

2023-02-16 09:23:38 CMG Hausa

A ranar Laraba 15 ga wata, ministan harkokin sufurin tarayyar Najeriya Alhaji Mu’azu Sambo ya ce, majalissar zartarwar kasar ta amince da gabatar da na’urorin sanya ido kan duk wani jirgin ruwa dake dakon kaya a kasar.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai dake fadar shugaban kasa, bayan fitowa daga taron majalissar zartarwar kasar da aka saba gudanarwa a duk ranar Laraba.

Alhaji Mu`azu Sambo ya ce, yanzu haka kasashen Afrika 26 ne ke amfani da irin wannan na’ura a tasoshinsu, wanda hakan yake bayar da damar kula da kayayyakin da ake shigowa da su ko kuma fitar da su daga kasashen.

Ya ce wannan tsari idan an fara shi gadan-gadan zai tabbatar da hakikanin gaskiya a wajen lissafin adadin abin da kasar ke samu daga cinikayyar da ake gudanarwa ta teku, bayan haka kuma zai iya daga darajar kudaden shigar da kasar ke samu a tasoshin ruwan ta zuwa dala miliyan 235 a duk shekara. (Garba Abdullahi Bagwai)