logo

HAUSA

Sin ta ba da agajin kayayyakin aikin jinya ga Syria

2023-02-09 14:12:21 CMG Hausa

Yau Alhamis, an fara jigilar kayayyakin aikin jinya da za su biya bukatun mutane 5000 daga birnin Beijing na kasar Sin zuwa kasar Syria, wadanda suka kasance agajin jerin farko da kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta samar wa yankunan kasar Syria, wadanda bala’in girgizar kasa ya ritsa da su.

Bayan barkewar mummunar girgizar kasa a kasashen Turkiye da Syria, a ranar Litinin da ta gabata, kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta fara daukar matakai ba tare da wani jinkiri ba. Ta riga ta ba kungiyoyin Red Crescent na kasashen 2 tallafin kudi, inda kowaccensu ta samu dalar Amurka dubu 200. Haka zalika, kungiyar na ci gaba da lura da bukatun da ake samu a yankunan kasashen da Iftila’in ya ritsa da su, tare da samar da dauki gwargwadon karfinta. (Bello Wang)