logo

HAUSA

‘Yan Najeriya da dama sun mutu sakamakon wani hari a Burkina Faso

2023-02-07 14:24:53 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da ‘yan kasarsa da dama sun mutu sakamakon wani hari da aka kai Burkina Faso.

A cikin wata sanarwar da ya gabatar, Buhari ya ce, wadannan ‘yan Najeriya na kan hanyarsu ne na harlartar wasu harkokin addini a kasar Senegal, inda motar da suke ciki ta gamu da harin, a lokacin da suka ratsa wani wuri dake Burkina Faso.

Buhari ya ce, ya nemi ma’aikatar harkokin wajen kasar da ta umurci ofishin jakadancin kasar dake Burkina Faso, don ya tuntubi gwamnatin kasar wajen ganin an gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu.

Sanarwar ba ta bayyana wuri da lokacin aukuwar harin da kuma hakikanin adadin mutanen da suka mutu ba, amma kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito jami’in kungiyar addini ta mamatan na cewa, a kalla ‘yan Najeriya 16 ne suka mutu.

Ministar harkokin wajen kasar Burkina Faso Olivia Rouamba ta ba da sanarwa a wannan rana cewa, kasar tana bin bahasin batun, ta ce, kwanan baya, gwamnatin kasar ta yi kashedin kada masu yawon shakatawa su ziyarci wasu wuraren dake arewacin kasar, saboda akwai yiwuwar gamuwa da hare-haren ‘yan bindiga. (Amina Xu)