logo

HAUSA

’Yan Najeriya sama da dubu daya ne aka dawo da su gida daga kasashe masu makwabtaka da Najeriya

2023-02-06 09:05:37 CMG Hausa

A ranar 5 ga wata yayin wani taron manema labarai da aka shirya a Kano dake arewacin Najeriya, hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ta tabbatar da karbar ’yan Najeriya 1,003 daga kasashen Libya, da Sudan, da Chadi da kuma Jamhuriyyar Nijar.

Babban jami’in shiyyar Kano na hukumar Dr. Nuraddeen Abdullahi ne ya tabbatar da hakan. Ya ce, an dawo da mutanen ne sakamakon shigar kasashen ba tare da izini ba a kokarinsu na tsallakawa Turai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Aikin maido da ’yan Najeriyar, an gudanar da shi ne bisa hadin gwiwa da hukumar lura da ’yan gudun hijira ta duniya, kuma an debo su ne daga Agadez a Jamhuriyyar Nijar da Sudan da Libya da kuma Chadi, inda aka sauke su a filin jirgin saman marigayi Malam Aminu Kano dake jihar Kano.

Babba jami’in hukumar ta Nema shiyyar Kano Dr. Nuraddeen Abdullahi ya ce, an yanke shawarar kai wa mutanen dauki ne wajen dawo da su gida sakamakon samun rahoton mawuyacin halin da suka shiga bayan sun gaza cimman burinsu na tsallakawa zuwa kasashen Turai domin neman abun duniya.

Ya ce dukkannin wadannan mutane an samu nasarar dawo da su ne a tsakanin watan Afirilu zuwa Disambar bara, inda 665 suka kasance magidanta Maza da Mata 113 sai kuma kananan yara 225 da suka kunshi maza da mata.

Dr. Nuraddeen ya ci gaba da cewa bayan an kammala tantance su, an gano cewa sun fito ne daga jahohin Katsina, da Kaduna, da Bauchi, da Sokoto, da Legos da kuma Kano.

A lokacin da suke bayani ga jami’an hukumar bayar da agajin gaggawar ta kasa, ’yan gudun hijirar sun ce sun fuskanci tsangwama da cin zarafi sosai daga hukumomin kasashen da suka yada zango, yayin da wasunsu ma suka rasa rayukan su a hanyar tafiya.

“Wadanda muka yi hira da su da yawa za ka ji suna da-na-sani zuwa domin abin da suke da shi da sun alkinta shi ma a Najeriya, abin da ake bukata kawai ka dage ka sadaukar da kanka ka nemi abin kanka babu abin da babu a kasar nan, ba ka da wata kasa da ta wuce kasarka, sun je dai sun ga abin da suka gani, ina fatan za su  koyi darasi.”

Dr. Nuraddeen Abdullahi ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara himmatuwa wajen wayar da kan jama’a game da illar dake tattare da irin wannan tafiya ta ganganci kawai domin neman abin duniya, sannan kuma akwai bukatar kara daukar tsauraran matakai na sa ido a kan iyakoki.

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)