Kasar Columbia ta koma aikin daukar sojoji mata bayan shekaru 30 da suka gabata
2023-02-06 09:47:50 CMG Hausa
Ga yadda hukumar sojin kasar Columbia take ba da ilmomin shiga rundunar soja ga wasu ’yan matan kasar a Bogota, fadar mulkin kasar. Yau shekaru 30 da suka gabata, kasar Columbia ta dakatar da daukar sojoji mata, amma a bana, kasar ta koma aikin daukar sojoji mata, ta yadda sojojin mata za su iya taka rawa da kuma bayar da gudummawarsu wajen sauke nauyin tsaron kasa, da kuma tabbatar da zaman lafiya da adalci, da kuma hakkin bil Adama a kasar. (Sanusi Chen)