An yabawa liyafar bikin fitilu da CMG ya shirya a ciki da wajen kasar Sin
2023-02-06 14:48:15 CMG Hausa
An watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na kasar Sin da CMG ya shirya a jiya, wato rana ta 15 a sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, inda liyafar ta samu yabo daga masu kallo a cikin gida da ma wajen kasar.
Da misalin karfe 8:00 na safiyar yau, jimilar wadanda suka kalli liyafar kai tsaye ta kafofi mabanbanta na tashar CMG ya kai miliyan 332, adadin wadanda suka kalla a kai tsaye ta kafofin sadarwa na zamani ya kai miliyan 176, haka kuma yawan wadanda suka kalla kai tsaye ta talabijin ya kai miliyan 156. (Fa’iza Mustapha)