logo

HAUSA

Ma’aikatar tsaron Sin ta bayyana matukar adawa da harbo balan balan din kasar Sin

2023-02-05 21:43:02 CMG Hausa

Ma’aikatar tsaron Sin ta bayyana matukar adawa da matakin Amurka, na harbo balan balan din kasar Sin ta ayyukan fararen hula maras matuki.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar Tan Kefei ya fitar a Lahadin nan, ta bayyana rashin amincewa da matakin Amurka, na yin amfani da karfin tuwo wajen kakkabo balan balan din.

Tan ya ce "Mun gabatar da matukar rashin amincewa da matakin na Amurka, kuma muna da ikon daukar matakan da suka wajaba na shawo kan makamancin wannan yanayi".  (Saminu Alhassan)