logo

HAUSA

Sin da Rasha za su karfafa hadin gwiwa a harkokin da suka shafi kasa da kasa

2023-02-04 20:32:06 CMG Hausa

Kasashen Sin da Rasha, sun amince su ci gaba da inganta tuntubar juna da hada hannu kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa tare da karfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar a yau Asabar.

Haka kuma, wannan ya biyo bayan ziyarar da mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Ma Zhaoxu ya kai Rasha tsakanin ranar 2 zuwa 3 ga wata, a wani mataki na tuntubar juna tsakanin ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu. Yayin ziyarar, Ma Zhaoxu ya gana da takwaransa na kasar Sergey Lavrov, kuma ya tattauna da mataimakan ministan da suka hada da Andrey Rudenko da Sergey Vershinin. (Fa’iza Mustapha)