logo

HAUSA

IMF: Tattalin arzikin Sin na bayar da gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya

2023-02-04 20:26:02 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya bayyana cewa, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai bayar da gudunmwar da ya kai kaso 1 bisa 4 na ci gaban tattalin arzikin duniya a bana.

A cewar IMF, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai karu a bana, bisa la’akari da farfadowar harkokin kasuwanci biyo bayan saukaka matakan yaki da COVID-19, wanda zai bunkasa tattalin arzikin duniya. Haka kuma, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai karu zuwa kaso 5.2 a bana, idan an kwatanta da kaso 3 na bara. (Fa’iza Mustapha)