logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga al’ummun kasa da kasa da su ci gaba da goyon bayan Iraki wajen yaki da ta’addanci

2023-02-03 14:12:17 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya yi kira ga al’ummun kasa da kasa, da su ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Iraki wajen yaki da ta’addanci, da kawar da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar kungiyar IS, da hana komawa da yaduwarsu, da kuma inganta sakamakon da aka samu wajen nuna adawa ga ta’addanci.

Dai Bing ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, a yayin taron da kwamitin tsaron majalissar ya gudanar game da batun Iraki. Dai Bing ya bayyana cewa, bangaren Sin na goyon bayan Iraki wajen kulla abota tare da kasashe makwabtanta, da tinkarar kalubalolin kasa da kasa tare.

Kaza lika bangaren Sin, ya yi kira ga bangarori daban daban da su mutunta ikon mallakar kasar Iraki, da ‘yancin kanta, da cikakkun yankunan kasar, da kuma warware damuwar tsaro ta hanyar yin hadin gwiwa tare da gwamnatin Iraki.(Safiyah Ma)