Sojoji sun ceto mutane 30 daga harin ‘yan bindiga a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya
2023-02-03 09:37:53 CMG Hausa
Kakakin rundunar sojojin Najeriya Musa Yahaya, ya ce dakarun rundunar sun yi nasarar ceton wasu mutane 30, bayan sun fatattaki gungun wasu ‘yan bindiga daga kan wata hanya dake kusa da kauyen Manini, na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a arewacin kasar.
Musa Yahaya, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce sojojin sun yi arangama da ‘yan fashin dajin ne yayin da suke aikin sintiri, inda suka hana su yin garkuwa da matafiyan dake hanyar.
Jami’in ya kara da cewa, bayan barin wuta tsakanin sojojin da bata-garin, sun yi nasarar tarwatsa ‘yan fashin tare da ceton daukacin matafiyan lami lafiya. (Saminu Alhassan)