logo

HAUSA

IOC Ya Wallafa Bayanin Murnar Cika Shekara 1 Da Gudanar Da Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Sanyi Ta Beijing

2023-02-02 15:57:41 CMG Hausa

Jiya Laraba 1 ga wata, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa wato IOC, ya wallafi wani bayani a muhimmin bangaren shafinsa na Internet, don murnar cika shekara guda, da gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.

Bayanin ya bayyana cewa, a matsayinta na birni na farko da ya shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi da lokacin sanyi, Beijing ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi mai kayatarwa a bara, tare da jawo hankalin al’ummun kasar kusan miliyan 350 da su shiga wasannin kankara da dusar kankara.

Bayanin ya kara da cewa, tun tuni kasar Sin ta kasance sabon wuri mai ci gaban wasannin kankara da dusar kankara, kafin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. A farkon shekarar 2021, akwai filayen kankara guda 654 a kasar Sin, tare da dakuna da filayen wasan gudun dusar kankara guda 803. Kwalejin nazarin harkokin yawon shakatawa na kasar Sin ya kiyasta cewa, a lokacin sanyi na shekarar 2024 zuwa ta 2025, yawan masu yawon shakatawa zai wuce miliyan 520, kana kudin shiga da za a samu zai wuce kudin Sin RMB yuan biliyan 720.

Bunkasar wasannin motsa jiki na lokacin sanyi mai armashi, ta kuma kyautata sassan zamantakewar al’ummar kasar Sin. Kamar yadda bayanin IOC ya bayyana, bunkasar wasannin motsa jiki na lokacin sanyi ta amfani lafiyar al’umma, da harkokin nishadi, da zamantakewar al’ummar kasa da tattalin arziki. Alal misali, wadanda ke zaune a kusa da filayen wasanni, sun samu guraben aikin yi misalin dubu 81, sakamakon gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. (Tasallah Yuan)