logo

HAUSA

An mikawa shugaban Iran daftarin dokar shigar kasar kungiyar SCO

2023-02-02 11:20:05 CMG Hausa

Kakakin majalissar dokokin kasar Iran Mohammad Baqer Qalibaf, ya mikawa shugaban kasar Ebrahim Raisi, wasika mai kunshe da daftarin dokar shigar kasar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, domin amincewarsa da kuma aiwatarwa.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya rawaito cewa, matakin ya biyo bayan sanarwar da kakakin majalissar tsarin mulkin kasar ya fitar ne a ranar Asabar, inda ya tabbatar da amincewar majalissar dokokin da kudurin shiga kungiyar ta SCO.

Shi ma kamfanin dillancin labarai na sashen shari’ar kasar Mizan, ya rawaito kakakin majalissar tsarin mulkin kasar Hadi Tahan Nazif na cewa, bayan nazartar kudurin dokar, majalissar ba ta samu wani dalili dake nuna sabani tsakanin dokar da ka’idojin addini da na kundin mulkin kasar ba.

A watan Nuwambar shekarar 2022 ne majalissar dokokin Iran, ta amince da daftarin dokar shigar kasar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da gagarumin rinjaye.

Yayin taro na 21 na jagororin kungiyar ta SCO da ya gudana a watan Satumban 2021 a birnin Dushanbe na kasar Tajikistan, aka bayyana amincewa da shigar da Iran kungiyar a matsayin cikakkiyar memba.(Saminu Alhassan)