logo

HAUSA

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Masu Kula Da Harkokin BRICS Karo Na 1 A Bana

2023-02-02 10:29:39 CMG Hausa

Jiya Labara 1 ga wata ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, kuma jami’in kasar mai kula da harkokin BRICS Ma Zhaoxu, ya halarci taron masu kula da harkokin BRICS karo na farko na shekarar 2023, wanda aka bude a lardin Limpopo na kasar Afirka ta Kudu.

A jawabinsa yayin taron, Ma ya waiwayi sakamakon da kasashe mambobin BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, da Sin da Afirka ta kudu suka cimma, a fannin hadin gwiwar siyasa, da kafa tsare-tsare da dai sauransu a shekarar 2022, lokacin da kasar Sin ta shugabanci BRICS.

Ya ce kasar Sin tana son yin kokari tare da Afirka ta Kudu, wadda ke shugabantar BRICS a bana, da sauran abokan BRICS wajen aiwatar da sakamako, da ra’ayi daya da aka cimma a yayin tarukan shugabannin BRICS, da zurfafa huldar abokantaka a tsakanin mambobin ta bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye ci gaban tsarin BRICS, da kara azama kan ci gaban hadin gwiwar BRICS mai inganci, da kara ba da gudummawa wajen samun zaman lafiya da bunkasa a duniya.

A cikin jawabinta ta kafar bidiyo, ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta ce, Afirka ta Kudu za ta ci gaba da himmantuwa wajen inganta hadin kai, da taimakawa juna tsakanin kasashe mambobin BRICS, da habaka hulda a tsakanin BRICS da sauran kasashe masu tasowa, da kafa oda da tsarin kasa da kasa mai adalci, a kokarin ba da gudummowar BRICS wajen samun wadata da kwanciyar hankali tare. (Tasallah Yuan)