logo

HAUSA

Nijeriya na fuskantar babbar barazanar yaduwar zazzabin Lassa

2023-02-01 10:28:51 CMG Hausa

Hukumomin lafiya a Nijeriya sun sanar da cewa, kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika, na fuskantar babbar barazanar yaduwar zazzabin Lassa.

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta kasar (NCDC), ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, ta kaddamar da cibiyar kai daukin gaggawa a mataki na 2, domin karfafa tafiyar da ayyukan tunkarar cutar a kasar yanzu haka, bayan nazartar barzanarta da kwararru da masu ruwa da tsaki suka yi a ranar 20 ga watan nan.

Bayan nazarin cutar an gano cewa, an samu karuwar wadanda aka tabbatar sun kamu da ita idan aka kwatanta da shekarun baya, haka zalika an samu karuwar barazanar yaduwar cutar a tsakanin ma’aikatan jinya da karuwar mace-mace sanadiyyarta.

A ranar 22 ga watan Junairu, an tabbatar da mutane 244 sun kamu da zazzabin Lassa a kasar, inda 37 daga ciki suka mutu, lamarin da ya sa yawan mace-macen da cutar ke haifarwa ya kai kaso 15.1. (Fa’iza Mustapha)