logo

HAUSA

Tattalin arzikin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya kyautatu fiye da hasashen da aka yi

2023-02-01 14:32:41 CMG Hausa

Bisa alkaluman farko da hukumar kididdigar kungiyar tarayyar Turai ta bayar a jiya Talata, a shekarar 2022, yawan GDPn yankin kasashe masu amfani da kudin EURO ya karu da kashi 3.5%, yayin da na kungiyar tarayyar Turai ya karu da kashi 3.6 cikin dari.

Masana sun bayyana cewa, yanayi mai dumi sosai da aka samu a lokacin hunturun bana ya saukaka matsalar karancin makamashi, a sa’i daya kuma, goyon bayan da bangaren kudi ke samu a wasu kasashen tarayyar Turai ya karu, haka kuma an kaucewa shiga matsalar tattalin arzikin, lamarin da ya kyautatu ba kamar yadda aka yi hasashe ba. Amma a halin yanzu, tattalin arzikin kasashe membobin tarayyar Turai da yawa bai karu sosai ba, sai dai hakan bai kawar da dukkan hadarin fadawa matsalar tattalin arziki ba, don haka babu makoma mai haske.(Safiyah Ma)