logo

HAUSA

AfDB ya yi alkawarin tallafawa tsarin noma mai jure matsalolin yanayi a Afrika

2023-02-01 10:52:20 CMG Hausa

Bankin raya nahiyar Afrika AfDB, ya ce zai ware wasu kudade musamman domin inganta tsarin noma irin na zamani mai jure matsalolin yanayi a nahiyar, da shawo kan matsalar karancin abinci da bunkasa kudin shiga a yankunan karkara.

Pascal Sanginga, manajan sashen kula da harkokin noma da masana’antu na bankin ne ya bayyana hakan. Yana mai cewa, bankin ya ware wasu karin kudi domin tabbatar da kananan manoma sun samu dabaru da fasahohi da abubuwan da ake bukata na jure matsalolin yanayi.

Bankin ya yi alkawarin ware a kalla dala biliyan 2 a kowacce shekara nan ba da dadewa ba, domin inganta noma irin na zamani mai jure yanayi a nahiyar ta hanyoyin noman rani da adana ruwan sama da kyautata hanyoyin isa kasuwanni da kayayyakin more rayuwa da samar da ingantattun irrai. (Fa’iza Mustapha)