logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Amsa Wasikar Da Daliban Makarantar Hungary Suka Aika Masa

2023-01-31 11:42:12 CMG Hausa

Kwanan baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya amsa wasikar da daliban makarantar koyon harsunan Sinanci da Hungary ta kasar Hungary suka aika masa, inda ya karfafa gwiwar matasan Hungary da su kara fahimtar kasar Sin da kasancewa a matsayin wadanda suka gada da raya sha’anin sada zumunta a tsakanin Sin da Hungary.

A watan Oktoban shekarar 2009 ne Xi Jinping, wanda shi ne mataimakin shugaban kasa a wancan lokaci, ya ziyarci makarantar a yayin da yake ziyarar aiki a kasar. A gabanin bikin Bazara na gargajiyar kasar Sin a bana, a madadin daukacin daliban makarantar, wasu daga cikinsu sun aika wa shugaba Xi Jinping da mai dakinsa shehun malama Peng Liyuan wasika, inda suka taya su murnar shiga sabuwar shekarar Zomo bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Sun kuma bayyana yadda suka dauki shekaru 12 suna koyon Sinanci a makarantar, tare da bayyana fatansu na yin karatu a jami’o’in kasar Sin, da ba da gudummawa wajen kyautata dankon zumunci a tsakanin kasashen 2. (Tasallah Yuan)