logo

HAUSA

Tattalin arzikin Habasha zai karu zuwa kaso 7.5 a shekarar kasafin kudi da ake ciki

2023-01-31 10:36:28 CMG Hausa

Ministar kula da tsare-tsare da raya kasa ta kasar Habasha, Fitsum Assefa, ta ce tattalin arzikin kasar zai karu zuwa kaso 7.5 bisa dari a shekarar kasafin kudi ta 2022/2023 da aka fara daga ranar 8 ga watan Yulin 2022.

Cikin shekarar kudi da ta gabata, wato ta 2021/2022, kasar ta gabashin Afrika ta samu karuwar kaso 6.4 a tattalin arzikinta.

Kamfanin dillancin labarai na Habasha ENA, ya ruwaito ministar na cewa, bangaren aikin gona shi ne ke kan gaba wajen ci gaba da raya kasar. Tana mai cewa, bangaren ya samu karuwar kaso 6.7 a cikin watanni 6 da suka gabata. Ta kara da cewa, bangaren na bayar da gagarumar taimako ga bunkasar tattalin arziki ta hanyar tallafawa harkokin cinikayyar kayayyakin da ake fitar da su daga kasar. (Fa’iza Mustapha)