logo

HAUSA

Hukumar WHO: cutar COVID-19 ita ce “batun kiwon lafiya dake jan hankalin al’ummun kasa da kasa”

2023-01-31 10:38:07 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar a jiya Litinin cewa, ko da yake akwai sauyi a yanayin yaduwar cutar COVID-19, har yanzu tana kasancewa kamar “batun kiwon lafiya dake jan hankalin al’ummun kasa da kasa.”

Kwamitin kula da ayyukan gaggawa na hukumar WHO ya kira taro na watanni uku-uku kan hasashen yanayin cutar COVID-19 a ranar 27 ga wata, inda mambobin kwamitin suka nuna damuwa game da hatsari mai dorewa da cutar COVID-19 ke kawowa, domin yawan mutuwar mutane da cutar ta haddasa ya fi na sauran cututtukan numfashi masu yaduwa yawa. Kuma akwai karancin alluran rigakafi a wasu kasashe masu karamin karfi da matsakaicin kudin shiga da kuma wasu rukunonin mutane masu saukin kamuwa da cutar, kana ba a tabbatar da ko za ta haifar da sabbin kwayoyin cuta ba ko a’a.

Kwamitin ya yi kira da a dauki matakan kiwon lafiyar jama’a mai dorewa. Wato da farko, a kokarin rage yawan mutanen da suke kamuwa da cutar da kuma wadanda take sanadin mutuwarsu. (Safiyah Ma)