logo

HAUSA

Najeriya ta karbi sakamakon rahoton binciken kwararru daga bankin duniya kan ambaliyar ruwa da ta afku a 2022

2023-01-30 10:15:47 CRI

Ministar ta ce, manufar amfani da wadannan kwararru da suke amfani da hanyoyin fasaha wajen gaggauta samar da hakikanin asara ta rayuka da dukiyoyi sakamakon annobar ambaliyar ruwan shi ne domin gwamanti ta samu tabbacin yawan mutanen da za ta rinka taimakawa cikin gaggawa ba tare da wani jan lokaci ba.

Hajiya Sadiya Umar ta ci gaba da cewa, a baya ana amfani da wata tsohuwar hanya ce wadda kuma take daukar lokaci kafin gwamnati ta samu sahihin kididdigar kaddarori da rayukan da suka salwanta irin wannan annoba, wanda a kan shafe a kalla watanni 6 kafin a samu sakamako sabanin wannan tsarin da ake amfani da hanyoyi da dabarun zamani wato GRADE wanda ke karkashin kulawar bankin duniya, da ba ya wuce kwanaki 14 yake fitar da sakamako.

Kamar yadda ta ce rahoton wadannan masana ya fayyace gaba dayan yanayin annobar da kuma tasirinta da adadin barnar da ta yi da kuma mutanen da ta shafa a sassan tarayyar Najeriya.

“Adadin mutanen da suka gamu da annobar ambaliyar ruwa ta bara a tsakanin watan Yuni zuwa Nuwamba sun kai tsakanin miliyan 4.4 zuwa miliyan 4.9, kaso biyu ke nan na adadin yawan al’ummar kasar, sannan kuma sama da hekta dubu dari 650 na kayan abinci rahoton ya nuna sun lalace wanda aka kiyasta kudin su kan dala biliyan 1.837 zuwa biliyan 2.7.”

Haka kuma ta fuskar tattalin arzikin kasa, rahoton ya nuna cewa, Najeriya ta yi asarar dala buliyan 6.68, sakamakon rushewar gidaje da lalacewar kaddarorin gwamnati da na masu zaman kansu da kuma filayen noma da dabbobi.

Hajiya Sadiya Umar Faruok ta kuma zayyana wasu daga cikin manyan dalilan da suka haddasa ambaliyar ruwa a shekarar bara a tarayyar Najeriya.

“Rashin bin tsarin zubar da dagwalon masana’antu da wasu kamfanoni ke fitarwa da rashin wadatattun magudanan ruwa a wasu garuruwan dake jihohin kasar sun taimaka sosai wajen haifar da ambaliyar ruwa a daukacin jihohin tarayyar Najeriya.”

Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi amfani da hanyoyin fasaha na bankin duniya a wata kasar Afrika dake yammacin Sahara wajen kimanta karfin ambaliyar ruwa da kuma adadin mutanen da abin ya shafa, kana da dukiyar da ta salwanta, a cikin ’yan kwanaki kalilan ba tare da an dauki tsawon lokaci ba.

Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)