logo

HAUSA

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 20 a kudancin Nijeriya

2023-01-30 11:17:58 CMG Hausa

Mutane 11 sun mutu sanadiyyar taho-mugamar da wata babbar mota da motar bas suka yi a jihar Ondo ta kudu maso yammacin Nijeriya.

Kwamandan hukumar kiyaye aukuwar haddura a jihar Ondo, Sikiru Alonge, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, babbar motar ta keta ka’idar hanya, lamarin da ya kaita ga yin taho-mugama da motar bas, a kan titin yankin Odigba na Jihar, da safiyar jiya Lahadi.

Ya kara da cewa, hatsarin ya yi sanadin gobarar da ta halaka fasinjoji 11 dake cikin bas din. Yana mai cewa, tuni aka kashe gobarar.

A wani labarin makamancin wannan, mutane 9 sun mutu, cikinsu har da yara 2, sanadiyyar faduwar wata babbar motar dakon kaya a kan wata motar bas, a jihar Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriyar.

Shugaban hukumar kula da agajin gaggawa na jihar, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya shaidawa manema labarai cewa, babbar motar dake dauke da kwantaina mai tsawo kafa 20, ta kwacewa direbanta ne yayin da take sauka daga kan gada.

Jami’in ya kara da cewa, ita kuma motar bas din na daukar fasinja ne a lokacin da lamarin ya auku. Yana mai cewa, an gano gawargwaki 9 a wajen aukuwar hatsarin. (Fa’iza Mustapha)