logo

HAUSA

AU ta yi kira da a gudanar da zabuka cikin lumana da zai kunshi kowa da kowa a fadin kasashen Afirka

2023-01-28 15:32:17 CMG HAUSA

 

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kira ga kasashen Afirka da suka shirya gudanar da zabuka a watanni 6 na farkon shekarar 2023, da su tabbatar da cewa an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali tare da damawa da kowa da kowa, don kawo karshen amon bindigogi a nahiyar Afirka.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar da kungiyar ta fitar na cewa, kwamitin ya kuma yi maraba da kokarin da kasashe mambobin kungiyar AU ke yi na shirya zabuka a watanni shida na farkon shekarar 2023, wato kasashen Benin, da Djibouti, da Nigeria, da Mauritania, da Guinea-Bissau da kasar Saliyo.

Ta kuma jaddada bukatar kara karfin hukumomin shari'a a fadin nahiyar, domin magance duk wata takaddamar zabe yadda ya kamata, da inganta hanyoyin tattaunawa, da cimma yarjejeniya da sassanta rigingimun da suka shafi zabe a tsakanin 'yan siyasa.(Ibrahim)