logo

HAUSA

An harba makaman roka a kudancin Israila

2023-01-27 16:24:30 CMG Hausa

A daren jiya Alhamis 26 ga watan nan ne aka kaddamar da hare-hare da wasu rokoki daga zirin Gaza, zuwa wasu yankunan da ke kan iyakar kudancin Isra'ila da zirin na Gaza, ciki har da Ashkelon.

Sojojin rundunar tsaron Isra'ila sun ce, na’urorin kakkabo makamai na Iron Dome na Isra'ila, sun yi nasarar kakkabo wasu rokoki guda biyu.

Tun da farko, da safiyar jiyan sojojin Isra'ila, sun kutsa cikin sansanin 'yan gudun hijira da ke Jenin, wani birni da ke arewacin gabar yamma da kogin Jordan, domin gudanar da samame, tare da yin arangama da Falasdinawa dake yankin, inda suka kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da wani farar hula. Nan take ne kuma Falasdinu ta sanar da dakatar da yarjejeniyar daidaita ayyukan tsaro da Isra'ila.

Kungiyoyin jam’iyyu daban daban, ciki har da kungiyar Hamas, sun yi barazanar mayar da martani, amma, rundunar sojojin tsaron Isra'ila ta ce a shirye take, ta tinkari duk wani irin yanayi, ciki har da tinkarar makamin roka da mai yiwuwa za a harba mata daga zirin Gaza. (Mai fassara: Bilkisu Xin)