logo

HAUSA

EU ta ce akwai bukatar hada kai da kasashen bakin haure na asali domin shawo kan kalubalen bakin hauren

2023-01-27 16:28:39 CMG Hausa

A jiya Alhamis 26 ga watan nan ne aka bude kwarya-kwaryar taron ministocin harkokin shari'a, da na cikin gida na kungiyar EU a birnin Stockholm, fadar mulkin kasar Sweden.

Ministoci mahalarta taron sun amince da gudanar da ingantaccen hadin gwiwa da kasashen asali na bakin haure, a ganinsu, halin da ake ciki game da bakin haure a Tarayyar Turai yana tayar da hankalin al’umma, saboda haka, akwai bukatar gaggawa ta karfafa ikon lura da kan iyakokin dake waje da na EU, da karfafa ikon mayar da bakin haure, da kuma hana kaura ba bisa ka'ida ba.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)