logo

HAUSA

Kamfanin CCECC ya kara samun kwangilar gina layin dogo a Legos

2023-01-25 15:28:30 CRI

A ranar Talata 24, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sheda bikin rattaba hannu kan wata sabuwar kwangilar gina layin dogo kashi na biyu a cikin Legos domin saukaka harkokin sufuri a cikin birnin.

Gwamnan jihar Legos da ’yan majalissar dokokin jihar da kwamashinoni da kuma shugaban kamfanin gine-gine na kasar Sin China Civil Engeneering Company, wato CCECC, Mr. Chen Sichang na daga cikin wadanda suka sheda bikin sanya hannun wanda ya gudana a sabuwar tashar jirgin kasa ta Blue Rail Line da aka kaddamar .

Sabon layin dogon jirgin kasan na Blue Rail Line an gina shi ne bisa tsarin hadin gwiwa da gwamnatin Legos da ’yan kasuwa.

Kamfanin gine-gine na kasar Sin shi ne ya aiwatar da aikin kan kudin dala miliyan 182 kwatankwacin kudin kasa Sin RMB biliyan 1.256.

Da yake jawabin maraba, mataimakin gwamnan jihar Legos Femi Hamzat ya ce, wanann sabon layin dogo na zamani da zai rinka sintiri a birnin na Legos, zai rika jigilar kusan fasinjoji 450 ne a duk minti daya yayin da a sa a guda aka kiyasta mutane 25,000 za su yi amfani da shi a harkokin sufurin su.

“Wannan layin dogo da aka bude a wannan rana ta Talata zai taimaka wajen rage wahalhalu na sufuri da jama’a ke fuskanta a birnin Legos saboda yawan cunkoson ababen hawa, sannan kuma zai bunkasa tattalin arzikin jihar, kana zai saka jihar ta Legos cikin jerin manyan birane na duniya, kamar yadda kuka sani bukatar mutane dai ita ce a gabanmu. A don haka wannan aiki an yi shi ne domin al’ummar jihar Legos. Mai girma shugaban kasa ina so ka ba ni dama kuma domin mika godiya ga dukkannin wadanda suka taimaka wajen tabbatar da wannan aiki musamman ma kai kanka shugaban kasa da kamfanin kasar Sin.”

Shi kuwa da yake nasa jawabin, jakadan kasar Sin wato Mr. Cui Jianchun cewa ya yi, “Zan yi amfani da wanann dama wajen sanar da wasu mahimman batutuwa guda 3 na ci gaba da shugaba Xi ya kirkiro da su domin ci gaban duniya. Na farko muradun raya kasashen duniya, na biyu kuma tabbatar da tsaro a duniya baki daya, sai na uku kuma shirin zuba jari na biliyoyin daloli karkashin shirin tafiya kan gwadabe guda wajen tallafawa tattalin arzikin kasashe wanda ake yi wa lakabi da BRI Initiative, amma dai abin da Sin ta fi fifitawa shi ne kara samuwar hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika. Mai girma shugaban kasa ina son na tabbatar maka cewa kudurce-kudurcen ci gaba guda 9 da shugaba Xi ya bujiro da su domin kasashen Afrika, Najeriya za ta amfana da manyan ayyuka har 15 daga kasar Sin. Ina da yakinin cewa muddin kasashen biyu za su yi aiki tare, tabbas kasar Sin za ta iya cimma burinta na kawata biranen Najeriya kamar yadda kasar Sin ta bunkasa a yanzu ta fuskar ababen more rayuwa. Ha’ila yau ina son na kara tabbatar wa Najeriya cewa nan da ’yan shekaru za mu iya cimma muradun nan guda 5 da kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya tanadar wadanda suka kushi hadin kai wajen bunkasar tattalin arziki, da hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro da diplomasiyya da yin aiki tare kana da bunkasa harkokin sadarwa tsakanin al`umma.”(Garba Abdullahi Bagwai)