logo

HAUSA

An fara aiki da sashen farko na layin dogon da Sin ta gina a Lagos

2023-01-25 16:50:01 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jagoranci kaddamar da sashen farko na layin dogon jiragen kasa masu amfani da lantarki, wanda kamfanin kasar Sin ya kammala ginawa a jihar Lagos dake kudancin kasar.

A jiya Talata ne shugaban na Najeriya tare da kusoshin gwamnati, da wakilai daga bangaren kasar Sin, suka kaddamar da layin dogon, wanda shi ne irin sa na farko a yammacin Afirka, da aka aiwatar karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Tun a shekarar 2010 ne dai kamfanin gine gine na CCECC, ya fara aiwatar da ginin sashen farko na layin dogon mai tsayin kilomita 13 da tashoshi 5, cikin jimillar layin dogon da zai kai kilomita 27 idan an kammala shi baki daya. Kuma da zarar komai ya daidaita, za a rika jigilar fasinjoji sama da 250,000, cikin jiragen kasan da za su yi zirga zirga kan sashen na farko.

Yayin kaddamar da fara amfani da layin dogon, shugaba Buhari, ya jinjinawa karkon aikin, da nagarta, da kuma dadin tafiyar jirgin kasan.

Kaza lika a lokacin kaddamar da fara amfani da sashen na farko, an kuma aza tubalin ginin sashe na 2 mai tsayin kilomita 14.  (Saminu Alhassan)