logo

HAUSA

Wani jirgin kasa ya sauka daga layin dogo a jihar Kogi dake yankin tsakiyar Najeriya

2023-01-24 15:32:08 CMG Hausa

Hukumar lura da safurin jiragen kasa a Najeriya NRC, ta tabbatar da aukuwar hadarin jirgin kasa a jihar Kogi ta yankin tsakiyar kasar.

NRC ta ce jirgin kasan ya goce daga layin dogon da yake bi ne, a kusa da garin Itakpe na jihar Kogi a ranar Lahadi, amma ba a samu rasuwa ko jikkatar fasinjoji ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in tsara ayyuka a hukumar ta NRC a jihar Sanni Abdulganiyu, ya ce jim kadan da aukuwar al’amarin, an aike da tawagar masu aikin ceto, an kuma kwashe daukacin fasinjoji da ma’aikatan jirgin kasan lami lafiya.

NRC ta ce ana gudanar da bincike game da aukuwar hadarin, wanda ya haifar da dakatar da zirga zirgar jirgin kasa dake bin layin dogon na jihar Kogi. (Saminu Alhassan)