logo

HAUSA

Najeriya ta fara amfani da ofishin cinikayyar kayayyakinta dake China

2023-01-23 11:17:32 CMG Hausa

Hukumar bunkasa harkokin cinikayyar kayayyaki zuwa kasashen ketare ta tarayyar Najeriya NEPC ta kaddamar da shirinta na fitar da kayan amfanin gona ta amfani da ofishinta dake kasar China.

Tun dai a watan Junin shekarar bara ne hukumar tare da hadin gwiwa da kamfanin samar da kayan amfanin gona na Zeenab Foods Limited suka kaddamar da shirin, inda suka samar da cibiyar kulla cinikayyar a kasar Sin kuma a nan ne za a rinka baje kolin kayan amfanin gonar da ake samarwa a Najeriya kafin raba su ga sauran kasashen duniya.

A ranar Lahadi 22 ga wata ne a rukunin masana`antu dake Idu a birnin Abuja aka kaddamar da fara amfani da ofishin, inda a yayin bikin  manajan daraktan kamfanin abinci na Zeenab Foods Mr Victor Ayamere yake cewa a tashin farko an fitar da kwantaina 20 na kayan amfanin gona ta tashar ruwan Onne dake jihar Rivers da kudinsu ya kai dolar miliyan 1.311.

Ya yi fatan cewa wannan tsarin hada-hadar fitar da kayan abinci zai kara bunkasa harkokin musayar kudaden waje a Najeriya.

Mr. Victor ya ci gaba da cewa kamfanin abinci na Zeenab Foods a matsayinsa na kamfanin da ya samu shedar gwamantin tarayyar Najeriya wajen fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen ketare tun a shekara ta 2022, yanzu haka ya bude dakin ajiyar kayan amfanin gona a kasar Sin, inda ya fara tura nau’ikan kayan gona da suka kunshi Citta da Ridi.

Ya ce, suna fatan nan da kwanaki 45 masu zuwa kamfanin zai sake auna kwantaina a kalla 300 na kayan gona zuwa ma’ajiyarsa dake kasar ta Sin.

A yayin bikin, wakilin kasar Sin Allen Zhang ya ce jimullar mu’amullar ciniki tsakanin kasar Sin da Najeriya ya kai dolar biliyan 26 a shekarar 2022, adadin da ya haura na kasar Ghana da Kenya har sau 4 yayin da ya ninka na Kamaru kuma sau 6. (Garba Abdullahi Bagwai)